A kwanakin baya ne dai shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya gabatar da wani sharhi dake cewa, yanzu haka kasar Sin da wasu kasashe na zantawa kan yarjejeniyar RECP. Kuma yarjejeniyar TPP da aka cimma matsaya kan ta karkashin jagorancin Amurka tana bin babban ma'auni na hada-hadar cinikayya, wanda hakan ya ba da tabbacin cewa, Amurkan ce za ta tsara ka'idojin cinikayyar duniya na karni 21, maimakon sauran kasashen duniya ciki har da kasar Sin.
A yayin taron manema labaru da aka shirya a Talatar nan, mista Hong Lei ya amsa tambaya kan wannan ra'ayin na shugaba Obama, yana mai cewa Amurka na daukar babban matsayi kan wannan batu, amma ba ta da damar yin hakan bisa doka. {Bilkisu}