Kafofin watsa labarun Koriya ta Kudu suna ganin cewa, Koriya ta Arewa ta yi hakan ne a matsayin martani ga atisayen soja mai lakabin "Foal Eagle" wanda yanzu haka kasashen Koriya ta Kudu da Amurka ke gudanarwa.
Firaministan Koriya ta Kudu kuma mukadashin shugaban kasar Hwang Kyo-ahn, ya kira taron tsaron kasa na gaggawa da safiyar wannan rana fadar gwamnati, inda da kakkausan harshe ya yi Allah wadai da matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na harba makamai masu linzami, ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa za ta hada kai sosai tare da kasashen duniya, wajen daukar mataki yadda ya kamata kan Koriya ta Arewan.
Wannan ne dai mataki na harba makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi a karo na 2 a baya bayan nan cikin wata guda. (Bilkisu)