Mai magana da yawun MDD Farhan Haq ya fada cewa, tawagar za ta duba yadda ma'aikatu da hukumonmin gwamnatin kasar suke gudanar da al'amurransu, domin nazartar irin tallafin da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa za su baiwa kasar, kana da nazartar wuraren dake bukatar tallafin ayyukan MDDr domin cigaban hukumonin kasar da kungiyoyin fararen hula dake kasar.
Haq, ya kara da cewa, tun a ranar Talata ne tawagar ta isa kasar ta Gambia, sannan a ranar Laraba ta gana da shugaban kasar Barrow, bayan ta gana da mataimakinsa, da ministan harkokin wajen kasar, da jami'an MDD dake aiki a Gambia, da kuma jami'an diplomasiyya dake aiki a kasar ta yammacin Afrika.
A ranar 19 ga watan Janairu ne aka rantsar da Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambian a ofishin jakadancin kasar ta Gambia dake Dakar, babbar birnin kasar Senegal. (Ahmad)