Dujarric, ya ce yayin zantawa da mambobin kwamitin na tsaro kai tsaye ta kafar bidiyo, Ibn Chambas, ya bayyana musu cewa ofishin sa na fatan ci gaba da goyon mayan matakan samun daidaito, da yafiya, tare da dinkewar sassan al'ummar Gambia.
Ya ce tuni tawagar UNOWAS ta girke dakarun ta a kasar, domin tabbatar da nasarar mika mulki ga zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ake fatan zai koma Gambia nan gaba a yau Alhamis.
Ana sa ran Mr. Barrow zai bar birnin Dakar na kasar Senegal, zuwa gida Gambia bisa rakiyar Mr. Chambas. (Saminu)