in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tanzaniya ya umarci jami'an tsaro da su yaki masu fataucin miyagun kwayoyi
2017-02-13 10:18:02 cri

Shugaba John Magufuli na kasar Tanzaniya ya umarci jami'an tsaron kasar da su kara daura damara don ganin sun kawar da masu fataucin miyagun kwayoyi kwata-kwata a cikin kasar.

Shugaba Magufuli, kana babban kwamandan asakawar kasar ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi jim kadan bayan rantsar da sabon babban kwamishinan yaki da miyagun kwayoyi na kasar Rogers William Siyanga.

Haka kuma shugaba Magufuli ya kira ga dukkan jami'an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai da dakarun tsaron kasar a yakin da ake yi da masu fataucin miyagun kwayoyi.

Ya kuma yabawa dukkan jagorori a sassan daban-daban na kasar wadanda suka fara yakar masu wannan mummunan sana'a ta hanyar bankado sunayen wadanda ake zargi da dillancin miyagun kwayoyin.

A ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekara ce shugaban na Tanzaniya ya nada wata sabuwar tawaga wadda za ta jagoranci hukumar yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, kwanaki biyu bayan da manyan jami'an kasar suka fitar da sunayen mutane 65 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi, sunayen da suka hada da 'yan siyasa da shugabannin addinai da hamshakan 'yan kasuwa.

Alkaluma na cewa, kimanin 'yan kasar Tanzaiya 1,007 aka tukuma da aikata laiffukan da ke da alaka da safarar miyagun kwayoyi, inda yanzu haka suke tsare a gidajen yari a kasashen daban-dabam na duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China