Jakadan kasar Ghana a kungiyar AU Albert Yankey, ya ce tallafin kudin zai karfafa ayyukan WFP wajen yaki da karancin abinci mai gina jiki, da samar da abinci ga 'yan makaranta a wuraren 'yan gudun hijira.
Mr. Yankey, wanda ya nazarci halin da ake ciki game da bukatun 'yan gudun hijira a Bagassola dake yankin na tafkin Chadi, ya ce ya yi imani da tasirin ayyukan bada agaji da WFP, tare da sauran hukumomin MDD ke bayarwa ga 'yan gudun hijira.
Al'ummun wannan yanki mai iyaka da kasashen Chadi, da Nijar, da Najeriya, da Kamaru, na fusknatar tashe tashen hankula daga mayakan Boko Haram. A kuma watan Janairun bara ne WFP ya kaddamar da shirin raba abinci mai gina jiki ga mutane da yawan su ya kai 130,000, adadin da ya kunshi 'yan janhuriyar Nijar su 6,500.(Saminu Alhassan)