Bayan shafe sa'o'i da shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz da takwaransa na kasar Guinea, Alpha Conde, da suka shiga-tsakani don warware rikicin kasar Gambia cikin lumana, Jammeh ya bayyana godiya ga jama'ar kasar, inda ya kuma tsaida kudurin mika mulki.
Jammeh ya bayyana cewa, ana iya warware dukkan matsalolin da ake fuskanta cikin lumana, kana ya yi imani da cewa, jama'ar kasashen Afirka za su iya cimma matsaya da kansu, don tabbatar da kafuwar demokuradiyya da bunkasar tattalin arziki da zamantakewa. (Zainab)