Makasudin wannan kundin doka, da shugabanni da gwamnatocin AU suka rattaba hannu kansa shi ne na yin rigakafi da murkushe manyan laifuffuka na cikin gida da na kasa da kasa musammun ma ta'addanci, fashin taku, sata da makamai a kan jiragen ruwa, fataucin miyagun kwayoyi, satar shiga sauran kasashe , fataucin mutane, da kamun kifi ba bisa doka ba da sauransu.
Kundin ya jaddada muhimmancin kiyaye muhalli gaba daya da muhallin ruwa, musammun ma a yankin kasashen dake bakin ruwa da tsibirai, har ma da bunkasa da karfafa dangantaka a fannonin fadakar da jama'a kan harkokin teku, rigakafin abubuwa na ba zata da kuma yaki da 'yan fashin taku.
Haka kuma zai taimaka wajen kafa hukumomi a cikin gida, shiyya da ma yankin nahiyar da suka dace da tabbatar aiwatar da nagartattun manufofi da suka cancanci bunkasa tsaron teku.
A cewar wannan kundin, kowace kasar dake ciki ta dauki niyyar cigaba da kokarinta ta hanyar daukar matakan da suka dace domin samar da ayyukan yi, rage talauci da kawar da kangin talauci, bada kwarin gwiwa wajen fadakar da jama'a kan batutuwan teku ta yadda za a kafa wani yanayin rayuwa da karfafa hadin kan jama'a ta hanyar aiwatar da wata siyasa mai kyau, da halartar kowa da adalci da zummar warware matsalolin tattalin arziki da na jama'a. (Maman Ada)