Wani fitaccen manazarci ya shawarci gwamnatin kasar Kenya da ta dauki darasi daga shirin yaki da rashawa da kasar Sin ke amfani da shi domin kaucewa barazanar rushewar tattalin arzikin a kasar, wacce ke gabashin Afrika.
Fasfesa Peter Kagwanja, babban jami'i ne a cibiyar tsara dabarun mulki ta Pan Afrika, wacce ke birnin Nairobi, ya fadi hakan ne cikin wani sharhi a wata jarida cewar, irin tsauraran dokokin da kasar Sin ke amfani da su wajen yake da rashawa, wani abin koyi ne ga kasashe masu tasowa don yakar miyagun halaye.
Da yake karin haske game da yadda cin hanci ka iya dakile samun kyakkyawar makoma ga Kenyan, Kagwanja, ya ce, kamata ya yi manyan jami'an gwamnatin kasar su dauki darasi daga kasar Sin na hallaka duk wanda aka samu da yin zagon kasa ga ci gaban kasar.
Kasar ta gabashin Afrika, ta kasance cikin jerin kasashen duniya dake fuskantar zambar kudade daga jami'an gwamnati.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ya fada a yayin wata ziyararsa zuwa Israel cewar, kasar na fama da matsalar cin hanci a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu.
Domin yaki da wannan muguwar dabi'a, Kagwanja ya ba da shawarar amfani da tsattsauran hukunci kan wadanda aka kama da laifin aikata rashawa a kasar kamar yadda kasar Sin ke hukunta masu irin wadannan laifuka.
Kasashen Sin da Kenya za su yi musayar dabaru wajen kakkabe laifukan da suka shafi rashawa.
Kagwanja, ya lura cewar, tsarin da shugaba Xi Jinping ke amfani da shi na yaki da rashawa, abin koyi ne ga kasar Kenya da sauran kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa da gwamnati mai tsabta.(Ahmad Fagam)