in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya aika sakon ta'aziya ga takwaransa na Turkiya
2017-01-03 09:13:24 cri

A jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan sakon ta'aziya dangane da harin ta'addancin da aka kai wani gidan rawa a birnin Istambul, harin da ya yi sanadiyar rayukan mutane a kalla 39.

A cikin sakon, shugaba Xi ya mika jaje ga shugaba Erdogan, da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su. Bugu da kari shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana Allah-wadai da duk wani nau'i na ta'addancin. Kuma kasar Sin a shirye take ta hada kai da kasar Turkiya da sauran kasashen duniya a kokarin da ake yi na kawar da duk wata barazanar ta'addanci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China