in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya zanta da sakatare-janar na MDD mai barin gado ta wayar tarho
2016-12-27 09:51:34 cri
A jiya Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da babban sakataren MDD mai barin gado Ban Ki-moon, inda ya yabawa mista Ban din game da kyawawan manufofinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaban duniya baki daya, kana da irin damammakin da ya baiwa kasar Sin wajen zurfafa mu'amala tsakanin MDD da kasar Sin a tsawon wa'adin aikinsa na shekarau 10 a matsayin babban sakataren MDD.

Shugaba Xi ya ce, Ban ya cimma nasarori masu yawa wajen aiwatar da manufofin MDD, kuma ya samu matukar yabo bisa irin dunbun nasarorin da ya cimma a lokacin aikinsa.

Shugaban kasar ya jaddada cewa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da MDD ya kai wani babban matsayi, bisa irin mu'amalar dake tsakanin bangarorin biyu, ya kara da cewa kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da sabon sakatare janar na MDD Antonio Guterres, domin ci gaba da karfafa hadin kan dake tsakanin kasar Sin da MDD.

Ban, wanda wa'adin aikinsa karo na biyu na shekaru 5 ke karewa a karshen wannan shekara, ya yaba da irin goyon bayan da kasar Sin ta ba shi a tsawon wa'adin aikinsa a matsayin babban magatakardan MDD.

Mista Ban ya ce, kasar Sin ta taka ma muhimmiyar rawa wajen ciyar da shirin nan na samar da dawwammen ci gaba na MDD, da inganta hadin gwiwa wajen samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu, da kuma ba da taimako wajen yaki da sauyin yanayi a duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China