in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiyya ta dora alhakin mutuwar jakadan Rasha kan magoya bayan Fetullah
2016-12-21 10:22:13 cri

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya shedawa takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta waya a jiya Talata cewa, kungiyar ta'addanci ta Fetullah wato (FETO), ita ce ke da alhakin hallaka jakadan kasar Rasha dake Turkiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu mallakar gwamnatin kasar ya rawaito cewa, a yayin tattaunawar tasu ta wayar hannu, mista Cavusoglu ya bayyana wa Kerry game yadda aka kashe jakadan na Rasha Andrey Karlov, wanda aka harbe shi da yammacin ranar Litinin.

Kerry ya gabatar da sakon ta'aziyya ga Cavusoglu, kana ya bayyana fargaba game da faruwar lamarin.

Manyan jami'an biyu, sun kuma tattauna game da taron tattaunawar da ya gudana a Moscow tsakanin ministocin kasashen wajen Rashar da Iran da Turkiyya.

An kashe jakadan na Rasha ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron baje koli da aka gudanar a birnin Ankara da yammacin ranar Litinin da ta gabata ta hanyar harbin bindiga.

Ministan shari'a na kasar Turkiyya Bekir Bozdag, ya bayyana lamarin a matsayin rashin kunya, da kuma zubar da kimar 'yan sandan kasar Turkiyyar a ce suna da hannu wajen hallaka jakadan na Rasha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China