in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi Allah wadai da kashe jakadan Rasha a Turkiyya
2016-12-21 09:41:43 cri

A jiya Talata gwamnatin kasar Sudan ta yi Allah wadai da kashe jakadan kasar Rasha a Turkiyya, wanda aka harbe har lahira a ranar Litinin da ta gabata a birnin Ankara.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fitar ta yi kakkausar suka game da kashe jakadan na Rasha a Turkiyya, Andrey Karlov, tare da nuna adawa kan duk wani nau'i na cin zarafin bil adama bisa kowane irin dalili ne kuwa.

Sanarwar ta kara da cewa, kisan jakadan na Rasha wani mummunan laifi ne na aikata cin zarafin bil adama, da kuma yin karan tsaye ga dokokin kasa da kasa.

Ma'aikatar harkokin wajen ta Sudan ta aike da ta'aziyya ga iyalan marigayi jakadan na Rasha, da gwamnatin kasar, da ma al'ummar kasar baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China