in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a arewa maso gabashin Najeriya
2016-12-12 09:47:17 cri
Jami'ai a Najeriya sun ce wasu 'yan kunar bakin wake su biyu sun mutu da safiyar jiya Lahadi a birnin Maiduguri ta jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA, Sani Datti, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan kunar bakin waken biyu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da boma boman dake jikinsu suka tarwatse a dai dai lokacin da suke yunkurin kutsawa cikin kasuwar Monday market dake tsakiyar birnin Maiduguri.

Kakakin hukumar ya ce, mutane 17 sun samu raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibitin kwararru na garin Maiduguri domin basu kulawa, kana ma'aikatan ceto da jami'an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru.

Ita dai kasuwar ta Monday market, ta sha fuskantar hare haren kunar bakin wake musamman a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a birnin na Maiduguiri, lamarin da ya haddasa salwantar rayukan daruruwan jama'a.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China