in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 16 sun mutu sakamakon harin da dakaru suka kai
2015-12-28 09:40:42 cri

Rahoranni daga Najeriya na cewa, a kwanan nan ne wasu dakaru suka kai farmaki a wani kauyen da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar Najeriya, harin da ya haddasa mutuwar mazauna kauyen 16.

Bayanai na cewa, da misalin karfe 7 na maraicen ranar 25 ga wata ne, wasu dakaru da ba a san asalinsu ba suka kutsa cikin kauyen Kimba na garin Biu da ke jihar ta Borno, inda suka kona gidajen jama'a, tare da kashe mazauna kauyen 16 ciki har da wasu yara, baya ga yin garkuwa da mazauna kauyen 6.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai farmakin. Amma rahoton na cewa, mai yiyuwa ne kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, ganin yadda kungiyar ta sha kai hare-haren ta'addanci a jihar ta Borno, wanda ta kasance tungar mayakan. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China