Wani kusa a gwamnatin kasar Kenya ya bayyana cewa, kasar za ta mai da hankali wajen bunkasa masana'antu domin cike gibi a fannin hada hadar kasuwancin.
Ministan ciniki da masana'antu da hadin gwiwa na kasar Adan Mohammad, ya shedawa 'yan jaridu a Nairobi cewa, a halin yanzu, adadin kayayyakin da kasar ke shigowa da su daga kasashen ketare ya ninka har sau uku idan aka kwatanta da wanda take fitarwa zuwa kasashen waje.
Muhammad ya kara da cewa, bunkasa ci gaban masana'antu zai taimakawa kasar Kenyan wajen rage gibi ta fuskar takaita shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.(Ahmad Fagam)