Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing domin fara ziyarar aiki a ketare da kuma halartar taron shugabannin APEC
Da safiyar Larabar nan 16 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasashen Ecuado, da Peru da kuma Chile bisa gayyatar da shugabannin kasashen uku suka yi masa inda zai gudanar da ziyarar aiki a hukunce.
Haka zalika, bisa gayyatar da shugaban kasar Peru Pedro Pablo Kuczynski Godard ya yi masa, Xi Jinping zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen yankin Asiya da Pasifik watau APEC karo na 24, taron da zai gudana a birnin Lima fadar mulkin kasar ta Peru. (Maryam)