in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kara wa juna sani kan karfafa zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel
2016-11-16 10:09:30 cri

Babban birnin kasar Togo, Lome na karbar bakuncin wani taron tuntubar juna na shiyyar kan matakan dake da nasaba da tsaron jama'a da kula da ajiyar makamai a yankin Sahel daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Nuwamban bana.

Taron kara wa juna sanin na cikin tsarin ayyuka na shirin tsaron jama'a da kula da ajiyar makamai (PSSM) a yankin Sahel, tare da hadin gwiwar tallafin kudi na kungiyar tarayyar Turai da cibiyar MDD kan harkokin karbe makamai (UNODA) zuwa ga kasashe shida na yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso, Nijeriya, Mauritaniya, Mali, Nijar da Chadi.

Cibiyar shiyya dake kula da zaman lafiya da karbe makamai a Afrika (UNREC) dake hedkwata a birnin Lome na kasar Togo ta aiwatar da shirin PSSM.

Haka kuma makasudinsa shi ne na taimakawa ga tsaro da zaman lafiya a yankin Sahel, ta hanyar kawo wata gudunmuwa ta yadda za a iya rage hadarin sumogal din kananan makamai da makamantansu da kuma harsasansu a cikin shiyyar, da kuma kyautata tsaron jama'a da kula da ajiyar makamai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China