in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karya lagon kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel
2016-09-15 13:07:20 cri
Wata majaliya daga sansanin dakarun kasar Faransa ta sanar da cewa, an ci galabar kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel, inda a halin yanzu ba za su iya yin tasiri na kaddamar da manyan hare hare ko su karbe iko da garuruwa ba a yankunan Sahel.

Francois-Xavier De Woillemont, sabon kwamandan sansanin dakarun Faransa na Barkhane, bayan wata ganawa da shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore a Ouagadougou, ya ce yanzu haka a yankin Sahel, babu wata kungiyar 'yan ta'adda da za ta iya kaddamar da munanan hare-hare. Ya ce wannnan ba yana nufin an magance matsalar gaba dayanta ba ne, sai dai matakan da tawagar dakarun soji na kasashe biyar G5, da dakarun Barkhane suke dauka yana ba da sakamako mai kyau, sabanin yadda wasu mutane ke tsammani.

Kwamandan na Faransa ya ce, dakarun na kasashen biyar G5 sun hada da Burkina Faso, Chadi, Mauritaniya, Nijer da Mali sai kuma dakarun na Barkhane sun samu nasarori masu yawa wajen fatattakan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Ya ce a halin yanzu, an karya lagon 'yan ta'adda, kuma ba su da wani katabus.

Mafi yawan kasashen yankin Sahel na fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin 'yan ta'adda, lamarin da ya tilastawa hukumomi a kasashen daukar matakan tabbatar da tsaro, tare da tallafin kasar Faransa. (Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China