Sauyin tattalin arzikin kasar Sin zai zama wani muhimmin ginshiki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, a cewar Chi Fulin, darektan cibiyar kawo sauye sauye da cigaba ta kasar Sin.
Da yake jawabi a yayin dandalin sauye sauye na kasar Sin da aka bude a ranar Asabar, mista Chi ya bayyana cewa gudummawar Sin ga tattalin arzikin duniya za ta tsaya ga kimanin kashi 30 cikin 100 a tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Tattalin arzikin duniya zai sami wata raguwar bunkasuwa a cikin shekaru masu zuwa duk tare da neman wani sabon daidaito, lamarin da zai haifar da sakamako kan sauyin tattalin arzikin kasar Sin, in ji mista Chi.
Ta wani bangare, a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arzki a duniya, sauye sauye da bunkasuwar tattalin arzikin Sin za su kawo wani babban tasiri ga tattalin arikin duniya. Gudummawar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ga tattalin arzikin duniya an kiyasta ta tsakanin kashi 25 cikin 100 da kashi 30 cikin 100, in ji jami'in. (Maman Ada)