Tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 6.7 cikin 100 a watanni hudun karshen shekarar nan ta 2016, wannan tagomashi da tattalin arzikin kasar ya samu tun daga watanni hudu na biyu na shekarar bana, alamu ne dake nuna cewa mai yiwuwa ne gwamnatin Sin ta cimma muradinta game da hasahen da ta yi na karuwar ma'aunin tattalin arzikin GDP na kasar a wannan shekara.
Alkaluman da hukumar kididdaga ta kasar Sin ta fitar a Larabar nan, sun nuna cewa, hasashen da gwamnatin kasar ta yi na samun karuwar tattalin arzikin daga kashi 6.5 zuwa 7 a shekarar 2016 ya tabbata. (Ahmad)