in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sun Yang na shirin lashe karin lambar yabo a gasar Olympics ta Tokyo
2016-09-28 19:45:16 cri
Fitaccen dan wasan linkayar kasar Sin Sun Yang, ya ce har yanzu yana ci gaba da atisaye, a wani mataki na tinkarar gasar Olympics ta gaba da za a gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan.

Sun, wanda ya lashe lambar zinari a gasar linkaya ta mita 200 da mita 400 a birnin Rio, ya ce har yanzu bai tsagaita ba da horon da yake samu, bisa burin sa na sake lashe lambar zinari a Tokyo, matakin da zai bashi damar kammala sana'ar sa da cikakkiyar nasara.

Sun dai na cikin 'yan wasan linkaya da suka halarci bikin karramawa da aka yiwa 'yan wasan na kasar Sin a Huangshan, wurin da a can ne ake gudanar da gasar kwararru ta 'yan wasan linkayar kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China