A ranar Lahadin da ta gabata ce firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ziyarci jagoran juyin-juya hali na kasar Cuba Fidel Castro a birnin Havana domin mika masa gaisuwar fatan alheri da tashi murnar cika shekaru 90, a madadin shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar da kuma daukacin jama'ar kasar Sin.
A yayin zantarwarsa da Mr Castro, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasashen biyu sun kulla jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa da suka shafi fannoni da dama. Sun kuma cimma matsaya daya kan ci gaba da karfafa zumuncin dake tsakanin Sin da Cuba da zurfafa hadin gwiwarsu a fannin raya kasa, da kuma nuna goyon baya ga juna wajen neman samun bunkasuwa ta hanyar da ta dace.
A nasa bangaren, Fidel Castro ya ce, a cikin shekaru 50 da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, kasar Sin ta samu ci gaba sosai, ya kuma yi farin ciki da irin ci gaban da kasar Sin ta samu. Kasar Cuba tana son kiyaye zaman lafiya da kara yin musayar ra'ayi da hadin gwiwa tare da kasar Sin.(Lami)