A jawabinsa shugaba Xi ya ce, ya yaba da irin nasarorin da kasar Cuba ta samu a cikin sama da shekaru 50 da suka gabata.
Ya kara da cewa, ya yi imanin al'ummar kasar Cuba za su kara samun nasarori a nan gaba karkashin jagorancin sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba (PCC) wadda Raul Castro ke zama babban sakatarenta.
Xi ya ce, dangantaka tsaanin Sin da Cuba ta jure canje-canjen da duniya ke fuskanta, kana kasashen biyu suna da ra'ayi daya kana suna la'akari da abubuwan da ke damun juna.
A nasa jawabin Valdes ya ce, bangaren Cuba ya yaba da dadadden zumuncin da ke tsakanin Cuba da Sin, kuma sabbin shugabannin kasar suna dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakanin jam'iyyun siyasu da kuma kasashen biyu. (Ibrahim)