Rahotannin baya bayan nan dake fitowa daga birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Congo Kinshasa, na cewa hankula sun fara kwantawa a birnin, bayan aukuwar tashe-tashen hankula da suka haddasa kisan wasu 'yan kasar. A daya bangaren kuma, ofishin jakadancin Sin dake kasar, da kungiyoyin Sinawa mazauna kasar, da kuma 'yan sanda sun yi hadin gwiwar ceto Sinawa su fiye da dari daga hannun 'yan bore.
A ranar Litinin ne dai tashe-tashen hankula masu tsanani suka barke a wasu sassa na birnin Kinshasan, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 17, ciki har da 'yan sanda 3.(Lami)