Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa a jiya Alhamis, inda aka nuna bakin ciki kan aikin gudanar da takardar tsarin hadin gwiwa na kiyaye zaman lafiya da tsaro a kasar Congo Kinshasa da yankunan gabar teku da aka kulla tun a shekarar 2013, an kuma ba da shawarwari kan batutuwan da suka shafi kiyaye zaman lafiya da yunkurin siyasa da hako makamashi ba bisa doka ba da kuma yanayin jin kai a yankin gabat teku.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na MDD ya jaddada cewa, dole ne a tarwatsa dukkan kungiyoyin tada kayar baya a gabashin kasar Congo Kinshasa, da ingiza kasashen Congo Kinshasa da Uganda da kuma Ruwanda su mika tsoffin dakarun da suka aikata laifin M23 koma kasashensu, da hana tilasta kananan yara shiga aikin soji, da sa kaimi ga kasashe daban daban da su shiga yunkurin shimfida zaman lafiya ta hanyar siyasa, da kuma katse hanyar ciniki ta dakaru wajen samu riba ta hanyar hako makamashi ba bisa doka ba.(Lami)