in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda a Kenya sun fara bincike game da badakalar gasar Olympic
2016-08-31 13:51:28 cri
Sashen binciken laifuka na rundunar 'yan sandan kasar Kenya ko DCI a takaice, ya fara gayyatar 'yan wasan da suka wakilci kasar a gasar Olympic da ta kammala a birnin Rio na kasar Brazil, domin jin ta bakin su game da badakalar da ta lullube tawagar kasar a wannan gasa.

Da yake tabbatar da hakan, dan wasan Javelin, wanda kuma ya ciwa kasar ta Kenya lambar Zinari a ajin maza Julius Yego, ya ce sashen na 'yan sanda ya tuntube shi, game da zargin da ake yiwa wasu manyan jami'an tawagar kasar na kin kula da 'yan wasa yadda ya kamata, da batun neman cin hanci daga wasu 'yan wasa da dai sauran su.

Hakan dai na zuwa ne kasa da kwana guda, bayan da ministan wasannin kasar Hassan Wario, ya bayyana rushe kwamitin gasar Olympic na kasar ko NOCK a takaice, aka kuma rufe helkwatar sa, bisa umarnin shugaban kasar Uhuru Kenyatta.

Shugaba Kenyatta dai ya yi umarni da a bincike dukkanin al'amuran da suka wakana kafin, da kuma lokacin gudanar gasar, da ma bayan kammalar ta.

An dai zargi jami'an NOCK da na ma'aikatar wasannin kasar, da saida wasu kaya da aka tanada domin jami'an tawagar kasar, yayin da a daya hannu ake zargin manajan tawagar 'yan wasan tseren kasar Major Michael Rotich mai ritaya, da wani koci mai suna John Anzrah, da laifin yiwa 'yan wasan kasar kashedin kauracewa shan kwayoyin kara kuzari, lokacin da za a yi musu gwaji, da nufin a basu na goro, da ma wasu laifuka masu alaka da rashawa.

An dai garkame kofar sakatariyar NOCK dake birnin Nairobi, yayin da ma'aikatan ta suka kauracewa ayyukan su, duk da furucin da sakataren kwamitin na NOCK Francis Paul ya yi, na cewa za su ci gaba da aiki duk da an rushe su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China