in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin shirya gasar wasannin nakasassu ta Rio zata raba tikiti ga kananan yara 30,000
2016-08-31 13:49:19 cri
Sama da yara 'yan makaranta dubu 30 ne kwamitin shirya gasar wasannin Rio zai basu kyautar tikiti na shiga gasar a wata mai zuwa, karkashin shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da kwamitin shirya gasar wasannin na Rio 2016.

Jami'an kafafen yada labarum kasar Brazil, wato Agencia Brasil sun bayyana cewa, daliban zasu samu kyautar kudaden zirga zirga, dana wuraren kwana, dana abinci rana, da kuma rigunan wasannin motsa jiki na nakasassu.

Za'a baiwa yaran da suke da nakasa fifiko wajen rabon tikitin.

Agencia Brasil ya ce; " manufar aiwatar da wannan shiri shine, domin baiwa kananan yara damar sanin al'amurran wasanni, da wasannin nakasassu"

A cikin wannan watan, kwamitin shirya wasannin Olympic, da gwamnatin kasar Brazil sun raba tikiti kimanin 55,000 ga yara 'yan makaranta a wasannin kwallon kafa, dana badminton, dana kwallon tebur, da wasannin dambe da dai dauransu.

Za'a gudanar da wasannin nakasassune tsakanin ranakun 7 zuwa 18 ga watan Satumba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China