
Rahotanni daga hukumar watsa labarai na ofishin kula da harkokin shugaban kasar sun ruwaito shugaban kasar Kyrgyzstan Atambayev, inda ya bukaci shugaban hukumar tsaron kasa da ministan harkokin cikin gidan kasar da su jagoranci gudanar da bincike kan wannan lamari, a sa'i daya kuma, ya bukaci gwamnatin kasar da hukumomin tsaron kasar da su bullo da matakan yaki da ta'addanci a babban birnin da sauran sassan kasar cikin sauri, ciki har da yadda za a kiyaye tsaron ofisoshin jakadancin kasashen ketare da ma'aikatansu dake kasar Kyrgyzstan
Bugu da kari, wani jami'in hukumar tsaron kasar ya bayyana cewa, maharin ya rasu sakamakon fashewar bama-baman, a halin yanzu, hukumomin da abin ya shafa suna kokarin tabbatar da asalin maharin, ta hanyar bincike kwayoyin halittar gado na DNA a gawarsa.
Kaza lika, hukumomin tsaron kasar suna yin bincike kan wuraren motar da maharin ya tuka ta taba zuwa a kasar Kyrgyzstan. (Maryam)




