
Kasar Sin ta nuna matukar bacin rai, tare da juyayin harin bam da aka kai kan ofishin jakadancin kasar dake kasar Kyrgyzstan. An dai kaiwa ofishin jakadancin na Sin dake birnin Bishkek hari ne da safiyar ranar Talata, da wata mota makare da bam, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar ma'aikatan ofishin su 3.
Da take karin haske game da lamarin a yayin taron manema labarai, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce tuni aka fara bincike game da wannan lamari, yayin da Sin ta mika bukatar ta ga Kyrgyzstan, ta daukar matakin kare rayukan Sinawa, da sauran ma'aikata dake aiki a ofishin jakadancin nata.
Ta ce Sin na kuma fatan Kyrgyzstan za ta gaggauta bincike, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya. (Saminu)




