Haka kuma, sanarwar ta ce, kafin gudanar da babban zaben shugaba a kasar ta Gabon, Ban Ki-moon ya yi kira ga al'ummomin Gabon da su aiwatar da hakkinsu yadda ya kamata, sabo da ana sa ran ganin babban zabe ya gudana cikin zaman lafiya, da samun amincewa daga bangarorin da abin ya shafa.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa, musamman ma 'yan takarar babban zaben da su kai zuciya nesa, da kuma kaucewa furta kalaman da za su janyo fitina tsakanin al'ummomin kasar, da aikace-aikacen da za su haddasa tashe-tashen hankula a wannan kasa, kana, ya kamata a kiyaye yanayin zaman lafiya a yayin babba zaben shugaban kasar, da kuma warware sabanin da mai yiyuwa za a fuskanta ta hanyar yin amfani da dokokin kasar.
Za a gudanar da babban zaben shugaban kasar Gabon a ran 27 ga watan nan da muke ciki, inda mutanen kasar za su zabi sabon shugaban kasar daga 'yan takadar da za su shiga zaben, ciki har da shugaban kasar na yanzu Ali-Ben Bongo Ondimba. (Maryam)




