Babban sakataren kungiyar Ahmad Allam-Mi, shi ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yana mai cewa tawagar za ta gudanar da ayyukanta ne karkashin jagorancin jakada Abou Moussa, tsohon jami'in jakadancin kasar Chadi, wanda kuma ya taba wakiltar MDD a kasar ta Gabon. ECCAS dai na fatan tawagar za ta sanya ido tare da tabbatar da kammalar zaben cikin lumana, ba kuma tare da wata rufa rufa ba.
Baya ga ECCAS, sauran kungiyoyin kasa da kasa da za su tura wakilan su yayin zaben na Gabon, sun hada da kungiyar hadin kan Afirka ta AU, da ta tarayyar Turai EU, da kuma kungiyar kasashe masu amfani da yaren Faransanci.
Shugaban kasar Gabon mai ci Ali Bongo Ondimba, kara da sauran 'yan takara 11 a babban zaben na wannan karo, ciki hadda tsohon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Jean Ping. (SAMINU)




