in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa 'yan wasan Real Madrid bisa nasarar da suka samu kan Real Sociedad
2016-08-24 13:29:29 cri
Kocin kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta Sifaniya Zinedine Zidane, ya bayyana farin cikin sa, game da nasarar da 'yan wasan sa suka samu kan kungiyar Real Sociedad, bayan da Madrid din ta doke Sociedad din da ci 3 da nema a wasan daren ranar Lahadi.

Zidane ya cirawa 'yan wasan sa irin su Gareth Bale tuta, wanda shi ne ya ciwa kungiyar kwallaye 2, yayin da matashin dan wasan kungiyar Marcos Asensio ya jefa kwallo ta uku.

Real Madrid dai ta bude wasan da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema, yayin da kuma James Rodriguez da Isco suka kasance a teburin canjin 'yan wasa, lamarin da ya nuna irin tarin kwararrun 'yan wasan da kungiyar ke alfahari da su.

Da yake karin haske game da yanayin zabar 'yan wasan da suka bude wa Real Madrid din wasa, koci Zidane ya ce ya amince Asensio ya fara shiga wasan, kuma dan wasan ya taka rawar gani, kamar yadda Isco da James ke yi. Ya ce abu ne mai wahala zabar 'yan wasa a kungiyar, duba da yadda ko wane dan wasa ke taka rawar gani yadda ya kamata. Duk da hakan koci Zidane ya ce babu wata matsala domin abu mafi muhimmanci shi ne nasarar kungiyar, ba wai wani dan wasa guda daya ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China