in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Djokovic ya lashe Nishikori tare da samun kofin Rogers
2016-08-02 16:29:52 cri
Shahararren dan wasan Tenis, wanda ya kasance na farko a teburin wasa na duniya, Novak Djokovic, ya lashe dan wasan kasar Japan Kei Nishikori da ci 6 da 3, da ci 7 da 5, a ranar Lahadin da ta gabata, ya kuma lashe kofin Rogers a karon 4.

Kofin ya kasance babban kambi na 30 da dan wasan kasar Serbia din ya samu, wanda ya sa yawan kambunansa suka haura na Rafael Nadal mai 28, da na Roger Federer mai 24, wadanda su ne fitattun 'yan wasa maza ta fuskar wasan tenis.

Banda hakan kuma, wannan nasara ta sa Djokovic samun kudin kyauta da yawansa ya kai dalar Amurka 782,525.

Dan wasan mai shekaru 29 a duniya, ya dade yana kan gaba a duniya a fannin fasahar wasan tenis, kuma ya riga ya yi makwanni 108 a jere yana matsayi na farko a duniya. A cikin wadannan makwannin, ya samu nasara a wasanni 6 daga cikin manyan kambuna guda 9 da aka fafata a manyan wasannin tenis da suka gudana a wurare daban daban na duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China