in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan 'yan gudun hijira na kasar Sudan ta Kudu sun isa Brazil
2016-08-02 16:29:10 cri
Daya daga cikin abubuwa masu janyo hankalin al'ummun duniya game da wasannin Olympics da za a fara a ranar Jumma'a shi ne, yadda aka kafa kungiyar 'yan gudun hijira domin 'yan wasan da suke gudun hijira a wasu kasashe su samu damar nuna kwarewarsu a yayin wasannin.

A ranar Jumma'ar da ta wuce, wasu 'yan wasa 'yan gudun hijira 'yan asalin kasar Sudan ta Kudu 5 sun isa birnin Rio. Cikinsu akwai Anjelina Nada Lohalith, wadda za ta halarci wasan tseren mita 1500, da sauran abokan wasanta 4, wadanda dukkansu a yanzu haka ke gudun hijira a kasar Kenya.

A cewar Anjelina, samun damar halartar wasannin Olympics na wannan karo na da muhimmanci matuka, ganin yadda 'yan wasan suka samu damar wakiltar dubun dubatar 'yan gudun hijira dake kasashe daban daban.

Kwamitin Olympics na kasa da kasa ya yanke shawarar kafa wata kungiyar musamman ta 'yan gudun hijira, bisa la'akari da yadda rikice-rikicen da ake fama da su a gabas ta tsakiya, da wasu yankunan Afirka suka tilasta wa mutanen watsi da muhallinsu, da yadda 'yan wasa masu dimbin yawa suke gudun hijira a kasashen waje. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China