in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar MEND a Najeriya ta amince da shiga tattaunawa da gwamnati
2016-07-25 10:17:24 cri

Babbar kungiya mai dauke da makamai a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya wato MEND ta ce, ta fara kwarya kwaryar tattaunawa da gwamnati da kuma kamfanonin mai dake yankunan da hukumomin tsaro na kasar.

Mai magana da yawun kungiyar Jomo Gbomo, ya fadi hakan cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, wannan kwarya kwaryar tattaunawar ita ce za ta share fagen shiga babbar tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyar ta MEND, wanda ake sa ran za ta zama sila na kawo karshen takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa game da rikicin yankin na Niger Delta mai arzikin mai.

A ranar Alhamis ne, shugaba Muhammadu Buhari ya fada a Abuja, babban birnin kasar cewa, za'a gudanar da tattaunawar ce tsakanin gwamnati da shugabannin kungiyar, ta hanyar kamfanonin mai da hukumomin tsaro na kasar domin lalibo hanyoyin da za su tabbatar da kawo karshen rikicin, tare da samun zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa tana ci gaba da yin nazari game shirin afuwa da ya gada daga gwamnatocin baya, domin aiwatar da batutuwan da ba'a aiwatar da su ba cikin yarjejeniyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China