Mataimakin daraktan hadaddiyar kungiyar tabbatar da adalci game da haraji ta Afirka, wato "Tax Justice Network Africa" Jason Braganza, shi ne ya bayyana hakan ga manema labaru a Nairobi, ya ce kasashen da suka ci gaba suna neman takaita ci gaban a tsakaninsu, wanda hakan babban koma baya ne ga kasashe masu tasowa.
Braganza, ya fada a lokacin taron na UNCTAD karo na 14 cewar, aiwatar da shirin na UNCTAD ga iya manyan kasashe babban hadari ne ga kasashe masu tasowa.
Ya bukaci hukumar ta MDD da ta fadada ayyukanta da yadda zai shafi shirin raya ci gaban karni na 2030.
Mataimakin babban daraktan ya kara da cewa, duk wani yunkurin na takaita ayyukan hukumar ta UNCTAD daga kasashe masu tasowa, hakan babbar illa ce ga kasashen Afrika.
Ya ce MDD tana da buri na musamman wajen taimakwa kasashe masu tasowa domin cimma muradansu na ci gaba.
Ya kara da cewar, hukumar na daya daga cikin hukumomin da suka yi hasashe game da yiwuwar fuskantar matsalar rikicin tattalin arzikin duniya shekaru 10 da suka wuce.
Ya ce wannan ne dalilin da ya sa kungiyar ta Afrika ta dukufa wajen ganin UNCTAD ba ta mayar da Afrika saniyar ware ba.
An kafa hukumar UNCTAD ne a shekarar 1964, da nufi ba da shawarwari game da hanyoyin da za su taimaka wajen ci gaban kasashe masu tasowa, sai dai Braganza ya lura cewar, hukumar ta saki layi game da makasudin kafata shekaru sama da 50 da suka wuce. (Ahmad Fagam)




