Wata babbar jami'ar kwamitin kula da harkokin kungiyar AU ta bayyana jiya Jumma'a, cewa kasar Sin na taka muhimmiyar rawa ga aikin raya muhimman ababen more rayuwar kasashen Afirka.
Elham Mohmood Ibrahim, wata jami'a mai kula da muhimman ababen more rayuwa da makamashi a kwamitin kula da harkokin kungiyar AU ta bayyana a yayin taron manema labarai da aka kira kafin kaddamar da taron koli na 27 na AU, cewar kasashen Afirka na son yin hadin gwiwa tare da dukkan abokansu wajen raya muhimman ababen more rayuwa. A ganinta, hadin kan Sin da Afirka ya dace da manufar samun nasara tare.
Ta kuma kara da cewa, a 'yan shekarun nan, kasar Sin ta sa hannu cikin ayyukan raya muhimman ababen more rayuwa na kasashen Afirka da yawa, kungiyar AU na maraba da irin hadin gwiwar Sin da Afirka a wannan fanni, kuma tana sa ran ganin gudanar da irin wadannan ayyuka nan gaba. (Kande Gao)




