A baya dai wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa dauki ba dadin na ranar Jumma'a, ya sabbaba rasuwar sojoji 30 yayin da kuma wasu sama da 70 suka jikkata.
Sai dai da yake mai da martani game da hakan a ranar Litinin, kakakin gwamnatin Nijar Assoumana Malam Issa, ya ce tabbas garin Bosso na karkashin ikon gwamnati. Ya ce mayakan na Boko Haram ba za su iya cin lagon dakarun sojin kasar ba.
Malam Issa ya kara da cewa mayakan na Boko Haram sun dai kai wa garin na Bosso hari ne, suka kuma lalata sassan sa, kafin daga bisani a tura karin sojoji, wadanda suka samu nasarar korar mayakan daga garin.
Kaza lika ya bayyana cewa a ranar Lahadi, ministan tsaron kasar Hassoumi Massaoudou ya ziyarci garin, inda ya gabatar da sakon jaje na shugaba Mahamadou Issoufou, da ma daukacin al'ummar kasar, bisa aukuwar wannan tashin hankali.
Ministan na tsaro ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin kasar, ta daukar fansar sojojin da suka rasa rayukansu a wannan balahira. (Saminu Hassan)