A cewar sanarwar, daruruwan mayakan Boko Haram sun kai hari a cikin daren Jumma'a zuwa Asabar kan wata tashar sanya ido da bincike ta sojoji dake Bosso. Ganin yadda mayakan suka yi amfani da manyan makamai, hakan ya tilastawa sojojin Nijar ja da baya.
A yayin wannan gumurzu, sojojin Nijar da Najeriya bakwai sun jikkata. A yayin da maharan su kuma suka tafi da nasu gawawwaki da wadanda suka jikkata da dama, in ji wannan sanarwa.
Mayar da martanin da jami'an tsaro da sojojin Nijar suka yi tun da safiyar ranar Asabar ya taimaka wajen kwace dukkan yankunan birnin Bosso. Kome ya lafa, kwanciyar hankali ya dawo a yankin, in ji sanarwar.
Ana cigaba da gudanar da aikin kakkabe yankin, tare da yin amfani da kayayyakin kasa dana sama domin kama da kawar da wadannan 'yan ta'adda.
A kalla a cikin makwanni uku, yankin Bosso yayi fama da hare haren ta'addanci har sau hudu, kuma na baya bayan nan ya faru a ranar 2 ga watan Yunin da ya gabata inda a lokacin fararen hula kusan 9 suka mutu tare da raunana wasu 13, daga cikinsu uku suka samu rauni mai tsanani, a Yebi dake Bosso. (Maman Ada)