Sanarwar ta bayyana cewa, tilas ne a gurfanar da wadanda suka kai hari da kuma wadanda suka taimaka wajen gudanar da shi a gaban kotu.
Kwamitin sulhun ya kuma ce kamata ya yi kasashen duniya su hada kai tare da gwamnatocin da abin ya shafa kamar yadda dokokin kasa da kasa da kudurorin da kwamitin sulhun MDD ya zartas suka tanada.
Bugu da kari, kwamitin sulhun ya yi kira da a dauki matakai don dakile dukkan hanyoyin da kungiyar Al-Shabaab da sauran kungiyoyin ta'addanci suke samun kudadensu, kana ya ce zai ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin da ake na shimfida zaman lafiya da samun sulhuntawa a kasar Somaliya.
A ranar Laraba ne wani bam da aka dana a cikin wata mota a kusa da otel din Amabassador dake birnin Mogadishu ya tashi, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 10, tare da raunata mutane 25. Kungiyar Al-Shabaab dai ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Zainab)