Ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Gao Hucheng, ya bayyana cewa, kasar Sin tana da tabbacin samun adadin kashi 7.5 cikin 100 da take burin cimmawa a cinikayyar ketare a wannan shekara, ganin yadda aka samu ingantuwar tattalin arzikin duniya da yin takara tsakanin masana'antun cikin gida.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a gefen taron shekara-shekera na majalisar wakilan jama'ar Sin.
Ya ce, ko da yake tattalin arzikin kasashe masu tasowa na fuskantar koma baya, muhimman abubuwan ake da su za su iya tunkarar matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, ta yadda tattalin arzikin nasu zai iya farfadowa a shekara 2014.
Alkaluman hukumar kwastan na nuna cewa, yawan kudaden da Sin ta samu a bangaren kayayyakin da ta shigo da su da wadanda ta fitar zuwa ketare sun kai dala tiriliyan 4, adadin da a karon farko ya kai dala tiriliyan 4.16 a shekarar 2013, wato kashi 7.6 cikin 100 a ko wace shekara. (Ibrahim)