in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin ya kai ziyara a kasar Luxembourg
2016-04-16 12:25:57 cri
Jiya ranar 15 ga wata, daya bayan daya sarkin Luxembourg Henri, da firaministan kasar Xavier Bettel sun gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, wanda ke ziyara a kasar.

A yayin ganawar, Sarki Henri ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Luxembourg da Sin na da dogon tarihi, kuma ta samu babban ci gaba a 'yan shekarun da suka wuce. Ya ce, ya taba kai ziyara a kasar Sin sau da yawa, babban ci gaba da Sin ta samu ya burge shi sosai. Kasashen biyu suna gudanar hadin kai yadda ya kamata a fannonin da suka shafi kudi, da jigilar kayayyaki ta hanyar zirga-zirgar jiragen sama, yana mai fatan za a kara samun sabon ci gaba kan hakikanin hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangaren Xavier Bettel ya bayyana cewa, kasashen Luxembourg da Sin suna nuna amincewa da juna, suna kasancewar ainihin aminai ga juna. Kasar Luxembourg tana jin dadi saboda ta kasance kasa ta farko a Turai wajen neman shiga bankin zuba jari ga ayyukan more rayuwa na Asiya na AIIB, tana kuma fatan karfafa hadin kai tare da Sin ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya, da kudi, da sufuri da dai sauransu, kana tana fatan zurfafa dangantakar hadin kai ta abokantaka a tsakaninta da Sin bisa tushen nuna girmama ga juna da zaman daidaituwa da samun moriyar juna.

Yang Jiechi ya yi bayani a yayin ganawar cewa, kasar Luxembourg ita ce muhimmiyar abokiyar hadin kai ta kasar Sin, a 'yan shekarun da suka wuce, kasashen biyu suna tsayawa tsayin daka kan nuna girmama ga juna, da amincewar juna, da zaman daidai wa daida, dangantakar dake tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya ta samu ci gaba sosai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China