Sin za ta hada gwiwa da kasar Afirka wajen gudanar da bikin baje koli na matsakaita da kananan kamfanonin duniya
A yau Jumma'a 8 ga wata ne mataimakin ministan masana'antu da sakwanni ta Sin Feng Fei, ya bayyana cewa kasar Sin za ta kaddamar da bikin baje koli na matsakaita da kananan kamfanonin duniya karo na 13, a ranar 10 ga watan Oktoba a birnin Guangzhou, kuma tuni aka gayyaci kasar Cote d'Ivoire domin a yi hadin gwiwar gudanar da bikin.
Wannan ne karo na farko da aka hada gwiwa da wata kasar Afirka wajen gudanar da bikin a cikin shekaru sama da 10 da suka wuce.
An ba da labari cewa, tun daga shekarar 2004, an riga an gudanar da bikin baje kolin sau 12 tare da cimma nasara. An kuma gayyaci kasashe da kungiyoyi sama da 10 domin shiga a dama da su a wannan biki.(Fatima)