Manajan bankin mai kula da harkokin Sin a yankin gabashin Afirka Cao Min ya yi bayani cewa, a matsayinsa na banki mafi girma a Afirka da aka kafa ya kusan shekaru 153, bankin Standard na kasar Afirka ta Kudu ya gano cewa, akwai fannoni da dama da Sin da kasashen Afirka za su yi hadin gwiwa a nan gaba. A shekarun baya baya nan, bankin ya kara gudanar da ayyuka tare da kasar Sin, da mai da kamfanonin Sin a matsayin muhimmin bangare da zai jawo jari ga bankin.
Cao Min ya bayyana cewa, tun a shekarar 2012 ne bankin Standard na kasar Afirka ta Kudu ya bullo da tsarin ajiya ko amfani da kudin Sin RMB a kasashen Afirka 20 ta yadda zai rika gudanar da hada-hada da kudin RMB. A halin yanzu, an fara amfani da wannan tsari a kasashen gabashin Afirka ciki har da Uganda, Kenya da dai sauransu. (Zainab)