Gwamnatin kasar Burundi ta dauki niyyar kai karar kasar Rwanda gaban kotun duniya (CIJ) bisa dalilan ta na ayyukan fitina, in ji mistan harkokin wajen kasar Burundi Alain Aime Nyamitwe.
Muna da shaidu da ke nuna cewa, Rwanda, a matsayin kasa, ta kawo lahani ga ikon mulkin kasarmu da mutuncin al'ummarmu. Muna da wannan 'yanci. A ko wane lokaci, za a iya tilasta mana kai kara kan kasar Rwanda gaban kuton CIJ, in ji mista Nyamitwe..
A cewar ministan, wannan kara kan Rwanda, za a gabatar da ita dalilin rashin kai ga cimma wani zaman lafiya da jituwa tsakanin kasashen biyu.
Wani dalili kuma shi ne kasashen Burundi da Rwanda dukkansu mambobi na MDD, kana sun amince da yin amfani hanyoyin da suka dace domin tabbatar da zaman tare cikin lumana. Amma kuma Rwanda ta yi biris da wadannan matakai, in ji mista Nyamitwe.
Kaddamar da daukar wannan aiki kan Rwanda wani mataki ne, ba wani shiri ba, in ji jami'in, tare da bayyana cewa, aiwatar da wannan mataki zai zo a lokacin da ya dace.
Mista Nyamitwe ya jaddada cewa, gwamnatin Burundi tana da shaidu dake nuna cewa, Rwanda ta yi yunkurin janyo wa Burundi fitina.
The Refugees International, wata kungiyar da ke kula da 'yan gudun hijira da ke Amurka, ta raiwato a shekarar da ta gabata cewar, ta gano gurbin sojoji a cikin sansanin 'yan gudun hijira da ka karbar mutanen Burundi a kasar Rwanda. (Maman Ada)