Wata tawagar kwararru da MDD ta turo kasar Burundi ta bayyana damuwa kan yadda ake keta hakkin bil-Adam a kasar Burundi.
Daya daga cikin kwararrun da suka ziyarci kasar ta Burundi Pablo de Greiff ya shaida wa manema labarai bayan kammala kashin farko na rangadin da suka kai kasar cewa, akwai jan aiki a dangane da batun da ya shafi kare hakkin bil-Adam a kasar.
Ya kuma nuna gamsuwa da yadda jami'an gwamnatin kasar suka nuna sha'awar tattaunawa da tawagar, duk da cewa, ana musgunawa kungiyoyin farare da suka himmatu wajen ganin an kare hakkin bil-Adam.
Mr Pablo ya yaba da hikimar da ke kunshe cikin yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawar kasar da aka cimma a shekara 2000 a birnin Arushan Tanzaniya, wadda ta hana gurfanar da wadanda suka tayar da rikicin kasar ta hanyar kafa hukumar kwatanta gaskiya da sasantawa.
Daga ranar 1 zuwa 8 ga wannan wata na Maris ne tawagar ta ziyarci kasar ta Burundi, inda ta gana da jami'an gwamnati, kungiyoyin al'umma da na fararen hula, da shugabannin addinai, shaidu da kuma wadanda aka ci zarafinsu a kasar.(Ibrahim)