in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DPRK ta sake harba wani makami mai linzami
2016-03-18 09:33:41 cri
A yau ne kasar Koriya ta Arewa DPRK ta harba wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango a yankin ruwan gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Koriya ta Kudu Yonhap ya ruwaito babban hafsan hafsoshin kasar yana cewa, an harba makamin mai linzamin ne daga yankin Sucheon da misalin karfe 5 da minti 55 na safe agogon wurin.

Bayanai na nuna cewa, makami mai linazami da kasar DPRK ta harba ta hanyar amfani da makamin harba na'urori masu linzami, ya yi tafiyar kimanin kilomita 800 kafin ya fada a yankin gabar tekun gabashin kasar. Hakan na tabbatar da cewa, makami mai linzami kirar Rodong ne.

Wannan shi ne karon farkon da DPRK ta harba irin wannan makami mai linzami tun ranar 26 ga watan Maris na shekara 2014, makamin da ta ce zai iya tarwatsa baki dayan yankin Koriya ta Kudu da manyan biranen kasar Japan.

Koriya ta Arewa dai ta harba makami mai linzami ne don nuna karfi da kuma bacin ranta kan atisayen sojin hadin gwiwa da kasashen Koriya ta Kudu da Amurka ke gudanarwa da kuma takunkumi mai tsauri da aka taba kakabawa kasar.

Kafin haka a ranar 10 ga watan Maris ma DPRK ta harba makamai masu linzami masu cin gajeren zango, kwanaki uku bayan fara aijisyen soji na hadin gwiwa tsakanin Koriya ta kudu da Amurka.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China