in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin tawagaogin kasashen Sin da Koriya ta Kudu na bangarorin 6 game da batun nukiliyar Koriya ta Arewa sun yi shawarwari a Seoul
2016-02-29 13:47:00 cri

Manzon musamman game da batun zirin Koriya na kasar Sin kuma shugaban tawagar kasar Sin game da yin shawarwari na bangarorin 6 kan batun nukiliya na Koriya ta Arewa Wu Dawei da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu, kuma wanda ke kulawa da batun samar da zaman lafiya a zirin Koriya na ma'aikatar kulawa da harkokin waje ta kasar Hwang Joon-kook sun yi shawarwari a ranar 28 ga wata a birnin Seoul dake kasar Koriya ta Kudu. Bayan shawarwarin, Wu Dawei ya fada wa wakilinmu cewa, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kai tsaye ba tare da rufa-rufa ba. Bangarorin biyu sun amince da nuna goyon baya ga sabon kudurin da kwamitin sulhu na M.D.D. zai bayar, bayan da Koriya ta Arewa ta yi sabon harbe. Bangarorin biyu sun nuna cewa, ya kamata bangarorin da abun ya shafa su yi kokari tare, don kiyaye zaman lafiya da karko da zirin Koriya.

A nasa bangare, bayan shawarwarin, Hwang Joon-kook ya ce, bangarorin biyu sun cimma matsaya guda game da yadda za a gudanar da kudurin kwamitin sulhu na M.D.D. da sa kaimi ga Koriya ta Arewa da ta kawar da makaman nukiliya, a sa'i daya kuma ya jaddada tuntubawa da hadin gwiwa a takaninsu.

Dadin dadawa kuma, Mr. Hwang ya ce, bangarorin biyu ba su ambaci batun kafa tsarin kare makamai masu linzami na THAAD a kasar. Game da batun daddale yarjejeniyar samar da zaman lafiya, Mr. Hwang ya ce, kawai nan gaba za a tattauna batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China