Kamfanonin kasar Sin dake gudanar da aiki a jihar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sun taimaka wajen ci gaba a shiyyar.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, shi ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya ce, kamfanonin sun ba da babbar gudumowa wajen ci gaban tattalin arzikin jihar, musamman wajen habaka ci gaban ilmi da aikin gona, da kimiyya da fasaha, da fannin kiwon lafiya, da kuma samar da kayayyakin more rayuwa.
Gwamna Masari ya kara da cewar, a shirye yake ya yi mu'amala da kamfanonin kasar Sin domin cin moriyar juna.
Kimanin bangarori hudu da suka hada da ilmi, da lafiya, da aikin gona, da kuma samar da ruwan sha ne gwamnatin Masara ta daura aniya kan su a Katsina, kuma gwamnan ya yi tabbacin ga kamfanonin kasar Sin cewar, za su kasance manya abokan huldar sa wajen aiwatar da ayyukan da aka sa a gaba.(Ahmad Fagam)